Gender Inclusive Framework and Theory (Hausa)
A Guide for Turning Theory into Practice
Daftarin Dake Bada Kulawa Ga Al’amuran Jinsi
Daftarin Juya Nazari Zuwa Aiki
Daftarin da ke bada kulawa ga jinsi kundi ne da akayi nazari a tsanake wajen samar da shi da zai saukaka yadda za’a rika bada kulawa tare da amfani da al’amuran da suka shafi jinsi yayin tsara wani shiri ko aiki. Saboda aikin samar da zaman lafiya ya dogara da nazartan al’amarin da yake dubawa, daftarin da ke bada kulawa ga jinsi ya gabatar da hanyoyi uku na nazartan al’amuran da suka shafi jinsi-mata, zaman lafiya da tsaro; halaye da dabi’un maza na kwarai; da asali ko alamomi da suka hadu da juna-an samar da su da nufin fuskantar al’amuarn jinsi dan kyautata tsara shirye-shiryen jaddada zaman lafiya.
Gabatarwa: Tsara Shirye-Shiryen Dake Bada Kulawa ga Jinsi
Tarzoma da tashin hankali na ruguza al’umma, suna lalata alaka tsakanin jama’a, musamman ma rawar da maza da mata kaiya takawa dama alakar dake tsakanin su. A wuraren da rikice-rikice suka shafa dama inda rikice-rikicen ka iya shafa, dole masu kokarin samar da zaman lafiya su gano tare da warware matsalolin dake haifar da tashin hankalin. Karuwar jefa matasa maza cikin daukar makamai da tashin hankali yana daga cikin abubuwan da ke rura wutar rikici, hakanan yawaitar fyade da cin zarafi da ya shafi jinsi matsala ce da ta shafi dukkan al’umma, kuma wannan matsala ka iya zama wani kurji da zai dami jama’a koda bayan tashin hankalin ya wuce. Ba’a shigarwa ko tsarma al’amuran jinsi acikin tsare-tsare da yawa dake kokarin karewa ko magance faruwar rikice-rikice. Bada kulawa ga kowane jinsi a lokacin tsarawa ko shirya yunkurin magance rikici yana da muhimmanci kuma shine hanya mafi kyau wajen kare afkuwar tarzoma da jaddada zaman lafiya, wannan ba mataki na biyu bane dan haka bai kamata a dauke shi a haka ba.1 Daftarin dake bada kulawa ga jinsi wajen tsare-tsare daftari ne mai sauki wanda kuma yayi la’akari da yadda ake tsarma jinsi acikin aikace-aikace ko shirye-shirye.
Taswirar Bada Kulawa Ga Jinsi Yayin Tsara Shirye-Shirye
- Yi Bayani akan Jinsi;
- Yi Jawabi Akan Alakar Dake Tsakanin Jinsi da Nau’o’in Tashin Hankali da Muhimmancin Su Ga Yunkurin Samar da Zaman Lafiya;
- Nazarci Hanyar Canja Dabi’ar Mutane Tare Da Zakulo Hanyoyin La’akari Da Jinsi a Shirye-Shirye; da
- Samar Da Tartibiyar Hanyar Shigar Da Jinsi Yayin Tsara Shirye-Shirye.