Daftarin Dake Bada Kulawa Ga Al’amuran Jinsi
Daftarin Juya Nazari Zuwa Aiki

Daftarin da ke bada kulawa ga jinsi kundi ne da akayi nazari a tsanake wajen samar da shi da zai saukaka yadda za’a rika bada kulawa tare da amfani da al’amuran da suka shafi jinsi yayin tsara wani shiri ko aiki. Saboda aikin samar da zaman lafiya ya dogara da nazartan al’amarin da yake dubawa, daftarin da ke bada kulawa ga jinsi ya gabatar da hanyoyi uku na nazartan al’amuran da suka shafi jinsi-mata, zaman lafiya da tsaro; halaye da dabi’un maza na kwarai; da asali ko alamomi da suka hadu da juna-an samar da su da nufin fuskantar al’amuarn jinsi dan kyautata tsara shirye-shiryen jaddada zaman lafiya.

Gabatarwa: Tsara Shirye-Shiryen Dake Bada Kulawa ga Jinsi

Tarzoma da tashin hankali na ruguza al’umma, suna lalata alaka tsakanin jama’a, musamman ma rawar da maza da mata kaiya takawa dama alakar dake tsakanin su. A wuraren da rikice-rikice suka shafa dama inda rikice-rikicen ka iya shafa, dole masu kokarin samar da zaman lafiya su gano tare da warware matsalolin dake haifar da tashin hankalin. Karuwar jefa matasa maza cikin daukar makamai da tashin hankali yana daga cikin abubuwan da ke rura wutar rikici, hakanan yawaitar fyade da cin zarafi da ya shafi jinsi matsala ce da ta shafi dukkan al’umma, kuma wannan matsala ka iya zama wani kurji da zai dami jama’a koda bayan tashin hankalin ya wuce. Ba’a shigarwa ko tsarma al’amuran jinsi acikin tsare-tsare da yawa dake kokarin karewa ko magance faruwar rikice-rikice. Bada kulawa ga kowane jinsi a lokacin tsarawa ko shirya yunkurin magance rikici yana da muhimmanci kuma shine hanya mafi kyau wajen kare afkuwar tarzoma da jaddada zaman lafiya, wannan ba mataki na biyu bane dan haka bai kamata a dauke shi a haka ba.1 Daftarin dake bada kulawa ga jinsi wajen tsare-tsare daftari ne mai sauki wanda kuma yayi la’akari da yadda ake tsarma jinsi acikin aikace-aikace ko shirye-shirye.

Taswirar Bada Kulawa Ga Jinsi Yayin Tsara Shirye-Shirye

  • Yi  Bayani akan Jinsi;
  • Yi Jawabi Akan Alakar Dake Tsakanin Jinsi da Nau’o’in Tashin Hankali da Muhimmancin Su Ga Yunkurin Samar da Zaman Lafiya;
  • Nazarci Hanyar Canja Dabi’ar Mutane Tare Da Zakulo Hanyoyin La’akari Da Jinsi a Shirye-Shirye; da
  • Samar Da Tartibiyar Hanyar Shigar Da Jinsi Yayin Tsara Shirye-Shirye.

Related Publications

La transition en Haïti ne peut réussir sans le leadership des femmes

La transition en Haïti ne peut réussir sans le leadership des femmes

Monday, October 28, 2024

Malgré l’instabilité politique et les bouleversements sociaux les plus graves de son histoire au cours de la dernière décennie, Haïti a désormais l’occasion d’aller de l’avant. La sélection d’un Premier ministre efficace par un Conseil présidentiel de transition offre au pays une chance de rétablir la sécurité et d’organiser des élections pour la première fois depuis 2016. Mais pour que les progrès soient durables, il faudra un mélange de leadership transitoire et de leadership transformationnel. Et cela signifie mobiliser et respecter le rôle essentiel des femmes, qui sont actuellement sous-représentées à tous les niveaux de gouvernement et d’influence.

Type: Analysis

Democracy & GovernanceGender

Haiti’s Transition Can’t Succeed Without Women’s Leadership

Haiti’s Transition Can’t Succeed Without Women’s Leadership

Monday, October 28, 2024

Despite facing some of the worst political instability and social upheaval in its history over the last decade, Haiti now has an opportunity to move forward. The selection of an effective prime minister by a Transitional Presidential Council offers the country a chance to restore security and hold elections for the first time since 2016. But for any progress to last, there will need to be a mix of transitional and transformational leadership. And that means mobilizing and respecting the essential role of women, who are currently underrepresented at all levels of government and influence.

Type: Analysis

Democracy & GovernanceGender

To Address Sexual Violence in Conflict, Don’t Overlook People with Disabilities

To Address Sexual Violence in Conflict, Don’t Overlook People with Disabilities

Wednesday, September 25, 2024

Sexual violence is a heinous crime that can affect anyone in conflict zones around the world. However, those with disabilities are often at greater risk of sexual violence than their counterparts without disabilities. Despite this, programs and policies for addressing conflict-related sexual violence (CRSV) rarely focus on how people with disabilities are uniquely affected, yet alone the best ways to prevent such violence, support survivors and seek justice.

Type: Analysis

GenderHuman Rights

View All Publications